A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, cikakken saƙon Mai girma Ayatullah al-Uzma Nuri Hamedani na goyon bayan rundunonin gwagwarmaya musamman Hizbullah, tare da la’antar kamawa da cin zarafin yan Shi’a a wasu kasashen yankin, shi ne kamar haka:
Bismillahir Rahmanir Rahim
Ina miƙa ta’aziyya kan shahadar Imam Ja’afar Sadiq (AS).
A cikin waɗannan kwanaki, da makiya, Sahyoniyawa da Amurka mai aikata laifuka suka kai hari ga Iran Musulma, lokaci guda suka kai mummunan hari ga al’ummar mazaluman Lebanon inda suka kashe da raunata wasu daga cikin su.
Dole ne dukkan ’yan uwa masu kishin ’yanci su la’anci wannan ta’addanci, kuma su goyi bayan rundunonin gwagwarmaya musamman wannan ƙungiya ta Hizbullah mai daraja. Mutanen Lebanon su sani cewa muna tare da su.
A gefe guda kuma, wasu rahotanni suna nuna cewa ana tsanantawa yan Shi’a a wasu kasashen Musulmi na yankin. Muna shawartar shugabannin wadannan kasashe da su daina bin turbar ma'abota girman kai da Sahyoniyawa, su yi tunanin martabar al’ummarsu, su kawo karshen wadannan tsanantawa da kamawa, kuma su kula da martabar al’ummar Musulunci gaba ɗaya.
"In tansurullaha yansurkum wa yuthabbit aqdamakum"
24 Farvardin 1405 (13 ga Afrilu, 2026)
Hussain Nuri Hamedani
Ra'ayinka